Zaben Donald Trump: Ra’ayin Ministocin Buhari ya rabu

Wasu Ministocin Buhari sun yi magana game da nasarar Donald Trump a zaben Amurka

Ministan noma Audu Ogbeh da Ministan Tsaro na Kasar Mansur Dan-Ali sun sha ban-ban na ra’ayi

Shugaba Buhari na Kasar ya taya sabon Shugaban Kasa Trump murna

Buhari in FEC meeting

Wasu daga cikin  Ministocin Buhari sun bayyana ra’ayinsu bayan da Donald Trump ya lashe zaben Kasar Amurka. A Ranar Laraba wasu daga cikin Ministocin suke magana game da halin da ‘Yan Najeriya za su kasance a Amurka da ma sauran Kasahen duniya bayan Donald Trump ya zama Shugaban Kasa.

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

Jaridar This Day ta rahoto Ministan Gona na Kasar, Audu Ogben yana mai mamakin yadda Donald Trump ya lashe zaben. Audu Ogbeh yace Sabon Shugaban kasa Donald Trump dan jari-hujja ne, zai kuma kashe Kasar Amurka.

KU KARANTA: Ministocin Buhari na fada

Audu Ogbeh yace dole Najeriya ta canza salon hulda da Kasashen waje idan har ‘Yan Kasar suka fuskanci wani barazana a waje. Minista Audu Ogben yace akwai babbar matsala tattare da nasarar Donald Trump a duniya. Shi kuwa Ministan Tsaro na Kasar, Birgediya-Janar Mansur Dan-Ali mai ritaya, cewa yayi dole a rungumi kaddara.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya sabon Shugaban Kasa da aka zaba Donald Trump murna a jiya, tun kafin nan ma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu ya aika da ta sa murnar. Farfesa Wole Soyinka dai yace ‘Yan Najeriya da masu gudun hijira ba za su ji da dadi ba a Amurka tun da Trump yaci.

The post Zaben Donald Trump: Ra’ayin Ministocin Buhari ya rabu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Zaben Donald Trump: Ra’ayin Ministocin Buhari ya rabu"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*