Zaben Donald Trump: Musulmai sun shiga Ha’ula’i

– Musulman duniya sun rikice bayan da Donald Trump ya samu nasara a zaben kasar Amurka

– Musulmai na tsoron za ayi ta kashe su a duniya

– Donald Trump yayi alkawarin hana Musulmai shiga Kasar Amurka

donald trump

 

 

 

 

 

 

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

Syed Chowdhury, wani Musulmi dan Kasar Bangladesh yace Amurkawa sun ja wa duniya bala’i, watau da suka zabi Donald Trump Shugaba. Musulmai fiye da Biliyan daya a duniya suna tunanin yadda abubuwan za su kasance bayan da Donald Trump ya lashe zaben Kasar Amurka.

Wata Baiwar Allah ta ke cewa ‘Ya ‘yan ta ka da su kara saka Hijabi daga yau, tun da Donald Trump yaci zabe. Wani yake cewa bai san yadda ‘Yan Gidan su za su yi ba. Alijah Diete, wani dan gwagwarmaya daga Indonesia yake cewa: ‘Ina tsoron za a shiga Yaki, Amurka tayi ta kashe mutane na Kasashen Musulmai

 KU KARANTA: Najeriya za ta samu makudan kudi

Wani Farfesa, Zuhairi Misrawi yace babu wadanda za su fi kowa murnar nasarar Trump, sai ‘Yan ta’adda na Kungiyar ISIL. Ishaq Khan yace ya so ace Hillary Clinton ce taci zabe, da Pakistan ta zauna lafiya. Khan yace Donald Trump fada da Musulmai zai yi, ban ji dadi da yaci ba. A Dubai ma dai, duk mutanen na cikin wani yanayi bayan da aka ce Trump yaci zabe.

Farfesa Wole Soyinka yace Najeriya da sauran Kasashen Afrika musamman na Yamma ba za su rika samun irin taimakon da suka rika samu a lokacin Shugaba Barrack Obama bat un da Trump yaci.

 

 

 

The post Zaben Donald Trump: Musulmai sun shiga Ha’ula’i appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Zaben Donald Trump: Musulmai sun shiga Ha’ula’i"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*