Yadda zamu lallasa Algeria-Mikel Obi

Jagoran yan wasan Super Eagles John Mikel Obi ya gargadi yan wasan da suyi takatsantsan a yayin fafatwarsu da kasar Algeri a wasan samu damar shiga gasar cin kofin duniya da zai gudana ranar Asabar 12 ga watan Nuwamba a garin Uyo, jihar Akwa Ibom.

vllkyt39obdnd7dtkg.6cfe1f58

Sai dai Mikel ya bayyana cewa yana da yakinin idan suka nuna jajircewa da dagiya, zasu lallasa abokan karawarsu. Mikel ya fadi haka ne yayin da yake jawabi ga yan jaridu a ranar Talata 8 ga watan Nuwamba. Yace:

“muna cikin yanayi mai kyau, kuma zamu cigaba da wasa kamar yadda muka saba, muna da kyau a fannin tsaron gida, sa’annan muna da kyau a gaba, ba laifi muna cin kwallaye. Dole ne mu cigaba da yin atisaye cikin ladabi da biyayya ga mai horar damu. Mun san Algeria suna da kyau, don haka dole sai mun dage don mu samu maki uku da ake bukata.

KU KARANTA: Osinbajo ya baiwa Super Eagles kwarin gwiwar buge Algeria

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

“dole ne mu fuskanci wasan yadda ya kamata don samun sakamako mai kyau. Yan wasan mu matasa ne yawancinsu, don haka muna da kyau. Ina ganin don dai mu zari kwallo mu ruga ba zai bamu wahala ba, zamu iya kai hari, muna da wannan kwarewar” inji Mikel.

Mikel ya cigaba da fadin “dole ne mu buga wasan nan har iya inda karfin mu ya kare, tare da yin takatsantsan.”

Najeriya zata yi kokarin cigaba da rike matsayin na daya a rukunin ta na B, matsayin data samu tun bayan data lallasa Zambia 2-1 a wasan zagaye na farko, inda ita kuma Algeria tayi canjaras 1-1 da kasar Kamaru.

Idan ba’a manta ba sabon kocin kasar Algeria Georges Leekens ya fito da jerin yan wasa masu karfi da zasu fafata da Najeriya, yan wasa kamar su Riyad Mahrez, Islam Slimani da sauransu.

The post Yadda zamu lallasa Algeria-Mikel Obi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Yadda zamu lallasa Algeria-Mikel Obi"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*