Wole Soyinka yayi amai ya lashe

– A da an rahoto cewa Farfesa Wole Soyinka yana mai cewa zai keta katin sa na zama Dan Kasar Amurka

– Mashahurin Farfesan yace a dakata sai an ga an rantsar da Trump bai yi hakan ba tukun

– Donald Trump dai ya ci zaben Shugaban Kasar Amurka

Wole-Soyinka (1)

 

 

 

 

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

 

Mashahurin Farfesan nan, kuma marubucin duniya, Wole Soyinka yace babu abin da zai sa keta katin sa na Kasar Amurka don wai Donald Trump ya ci zabe. Farfesa Wole Soyinka yace ai dama cewa yayi zai keta katin sa idan har an rantsar da Trump a matsayin Shugaban Kasar Amurkar.

Wole Soyinka yace masu jiran sa ya keta katin sa na zama dan Kasar Amurka sai su kara dakatawa don har yanzu ba a nada Donald Trump ba. Mashahurin Marubucin Afrikan yayi dauki wannan alkawari ne a farkon watan nan da yaje Kasar Ingila, inda yayi lacca ga daliban Jami’ar Oxford.

KU KARANTA: Zaben Amurka: Trump ya lashe

Farfesa Wole Soyinka yace idan har Trump ya zama Shugaban Kasar Amurka, to zai keta katin sa na zama dan Kasar. Wole Soyinka yace zai yi wahala Trump yaci zaben, yace abu ne mai wahalan gaske, sai ga shi kuma Donald Trump ya bada mamaki. Wole Soyinka yace ana sanar da cewa Trump yayi nasara, ‘zan tattara in dawo gida, in kuma keta kati na’.

Wole Soyinka yace idan har Donald Trump yaci zabe, sai sun kara neman sabon izinin shiga Kasar Amurka, yace babu dalili.

 

The post Wole Soyinka yayi amai ya lashe appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Wole Soyinka yayi amai ya lashe"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*