Wayyo! Wani babban iblila’i ya afkawa kungiyar Arsenal

– Dan kwallon Arsenal, Alexis Sanchez, ya yi rauni a lokacin da yake yin atisaye a tawagar kwallon kafa ta Chile

– Sanchez mai shekara 27, ba zai buga wa Chile wasan shiga gasar cin kofin duniya da za ta yi da Colombia a ranar Alhamis ba

Alexis Sanchez

Alexis Sanchez

Sai dai likitocin tawagar Chile sun ce, dan kwallon zai iya murmurewa ya kuma buga wa kasar karawar da za ta karbi bakuncin Uruguay a ranar Talata.

Sanchez wanda ya ci wa Arsenal kwallaye takwas a kakar wasannin bana, ya buga wa kungiyar wasan da ta yi kunnen doki 1-1 da Tottenham a ranar Lahadi a gasar Premier.

KU KARANTA: Kurkuku 5 masu hadarin gaske a Najeriya, na 3 zai baka tsoro

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

Arsenal wadda ke mataki na hudu a kan teburin Premier, za ta ziyarci Manchester United a ranar 19 ga watan Nuwamba a gasar Premier wasannin mako na 12.

A wani labarin makamancin wannan kuma, Likitocin Real Madrid sun tabbatar da cewar dan kwallon tawagar Jamus, Toni Kross, ya yi rauni. Dan kwallon ya yi rauni ne a karawar da Madrid ta ci Leganes 3-0 a ranar Lahadi a gasar La Liga da suka fafata.

A makon jiya ne, Toni Kross, ya sabunta yarjejeniyarsa da Real Madrid domin ci gaba da buga mata tamaula zuwa 2022. Dan kwallon mai shekara 26, wanda ya koma Bernabeu daga Bayern Munich a shekara 2014, ya ci wa Madrid kwallaye hudu a wasanni 108 da ya buga mata

A wani labarin kuma, Cristiano Ronaldo ya ce zai iya ci gaba da taka leda a kungiyar zuwa shekara 10, idan yarjejeniyar da ya sake kullawa da kungiyar ta kare. Kwantiragin Ronaldo mai shekara 31, da Real Madrid na shirin karewa a watan Yunin 2018, amma ya tsawaita ta, inda zai kai karshen kakar wasan 2021.

Dan kwallon na tawagar Portugal ya ce ba wannan ba ne karo na karshe da zai tsawaita yarjejeniyar ci gaba da wasa a Madrid, yana fatan sai ya kai shekara 41 kafin ya yi ritaya. Ronaldo ya ci kwallaye 371 tun lokacin da ya koma Madrid da taka-leda daga Manchester United a shekarar 2009.

The post Wayyo! Wani babban iblila’i ya afkawa kungiyar Arsenal appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Wayyo! Wani babban iblila’i ya afkawa kungiyar Arsenal"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*