Rikici: Gwamna ya tunbuke wani Sarki

– Gwamnatin jihar Edo ta tsige wani Sarki daga cikin Sarakunan garin

– Gwamnatin Adams Oshiomole ta tunbuke Mai girma Anselm Eidenojie

– Wannan abu ya jawo rikici, yanzu haka Sarkin yam aka karar Gwamna a Kotu

Sarki Anselm Eidenojie

Sarki Anselm Eidenojie

 

 

 

 

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

 

 

Gwamnatin jihar Edo karkashin Gwamna Adams Oshiomole ta tsige wani daga cikin masu Sarautar Kasar. Gwamnan ya tsige mai martaba Sarki Anselm Eidenojie. Mai Girma Anselm Eidenojie shi yake rike da Kasar Uromi da ke Yankin Arewacin Esan na Jihar Edo. Ana zargin mai martaba da aikata wasu laifi a baya.

An dai tabbatar da tsige Mai Sarautar ne a wata wasika da Gwamna ya aika ta Sakataren sa a jiya, 9 ga Wata. Dama can a baya, an dakatar da Sarkin. Wasikar tace ana sanar da Sarkin cewa an tabbatar da matakin da aka dauka a watan Jiya, don haka yanzu an tunbuke sa daga kujerar sa ta sarauta.

KU KARANTA: Sarki na Benin ya yabawa Shugaba Buhari

Sarkin dai yace ba zai yadda da wannan ba, don haka ya jefa karar Gwamna a Kotu. Sarkin yace an keta masa hakki. Sarki Anselm Eidenojie na Kasar Uromi ya kuma kai karar Mataimakin Sufeta-Janar na ‘Yan Sanda da ke Yankin, Ms. Okoebor Mathew Okoebor. Mai martaba Sarki yace ba za ta sabu ba.

A baya dai an dakatar da Sarki Anselm Eidenojie bayan da ya ki amsa sammaci. Gwaman yace Tsarin mulkin Kasa, ya ba da ikon sauke duk wani mai sarauta da ya saba. Yanzu haka dai ana ta zanga-zanga a Yankin.

The post Rikici: Gwamna ya tunbuke wani Sarki appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Rikici: Gwamna ya tunbuke wani Sarki"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*