Muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da sabon alkalin alkalai na tarayya, Walter Onnoghen

– A yau Alhamis ne, ake sa ran Shugaba Buhari Zai Rantsar da Mai Shari’a, Walter Nkanu Onnoghen a matsayin sabon Alkalin Alkalai na tarayya.

– Wata majiya ta tabbatar da cewa an kammala duk wasu shirye shirye na bikin rantsarwar wanda aka tsara gudanar da shi a zauren majalisar ministoci da ke Fadar Shugaban kasa, wannan mataki na rantsar da Walter Onnghen ya biyo bayan yin ritaya ne da Alkalin Alkalai, Mai Shari’a Mahmud Muhammad zai yi ne a yau Alhamis.

Hon. Justice W.S. Nkanu Onnoghen CFR

A yayin da Babban Mai Shari’a na Kasa, Mahmud Mohammed ke shirin yin ritaya daga aiki, hukumar kula da kotuna ta kasa ta gabatar da Mai Shari’a Walter Onnoghen a matsayin wanda zai maye gurbin kujerar.

NAIJ.com Hausa ta zakulo ma masu karatun mu wasu daga cikin Muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da Onnoghen kamar haka:

(1) Shi dai, Walter Onnoghen shi ne babba a jerin alkalan kotun koli ta kasa kuma a bisa tsarin mulki wanda ke kan gaba a shekarun fara aiki shi ne ke zaman Alkalin Alkalai na Kasa.

(2) An haife shi ne a garin Okurike da ke karamar hukumar Biase a jihar Cross Rivers a shekarar 1950 kuma an zabe shi a matsayin Alkalin kotun koli na kasa a shekarar 2005.

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

Karanta kuma: Didajen yari 5 masu hadarin gaske a Najeriya

Har ilayau a wani labarin kuma, Hukumar hana fasa kwabri ta Najeriya,Kwastam ta soma raba wasu kayakin da aka kama a hannun yan sumogal, ga al’ummomin da rikicin Boko Haram ya shafa a arewa maso gabashin Najeriya.

Dubban jama’a ne dai rikicin Boko Haram da aka shafe fiye da shekaru shida ana fama da shi,ya shafa,musamman a jihohin Adamawa,Borno da kuma jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya.

Wannan ne dai karon farko da hukumar ta kwastam ke raba wadannan kayakin tallafin da kanta a jihar Adamawa,daya daga cikin jihohin da rikicin Boko Haram ya shafa.

Kayakin sun hada da abinci,sutura da kuma sabulai,inda aka rabawa al’ummomin da rikicin Boko Haram ya shafa a kananan hukumomi bakwai da a baya suka fada hannun yan bindiga masu tada kayar bayan na Boko Haram,dama sansanonin yan gudun hijira dake jihar Adamawa.

Iya Abubakar shi ne mataimakin shugaban hukumar ta kwastam ,da ya wakilici shugaban hukumar,yace wadannan kayaki na ko cikin kayakin da hukumar ta kame,don haka ta kawo a rabawa wadanda rikicin ya shafa.

The post Muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da sabon alkalin alkalai na tarayya, Walter Onnoghen appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da sabon alkalin alkalai na tarayya, Walter Onnoghen"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*