Muhimman abubuwa 4 da wasu yan Arewa suka fada a kan Shugaba Buhari (Hotuna)

Hukumar NAIJ.com tayi hira da wasu yan Arewa mazauna jihar Lagas, inda ta ji ra’ayinsu game da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wadannan yan Arewa dai sun nuna jin dadinsu game da gwamnatin shugaba Buhari, inda suka ja hankalin yan Najeriya kan su daina nuna gazawa da wannan gwamnati, domin abubuwan dake faruwa bayinta bane. Sun kuma bayyana cewa babu abunda gwamnati tafi bukata a yanzu daga al’ummanta illa addu’a, hakuri da kuma juriya.

Ga wasu muhimman abubuwa guda 4 da suka hankaltar da yan Najeriya a kai game da gwamnatin Buhari:

KU KARANTA KUMA: Kungiyoyin Mafarauta na samun horo kan Boko Haram

1. Buhari na bukatar addu’a

Yan arewa

Muna fatan dukkan masu zagin shugaban kasa Muhammadu Buhari zasu daina domin ba laifinsa bane halin da kasa ke ciki, duk abunda ubangiji ya tsara babu makawa sai ya faru, abunda gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke bukata a yanzu shine addu’a daga al’umman kasar baki daya.

2. Hakuri daga yan Najeriya

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

Yan arewa

Tabbas yan Najeriya na cikin wani irin yanayi a yanzu, amma muna kyautata zaton komai zaiyi daidai nan bada jimawa ba. Sannan kuma muna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara kaimi gurin ganin rayuwar talakawa ya inganta ta hanyar sama masu abubuwan yi ta yadda zasu yi dogaro da kai.

KU KARANTA KUMA: Tinubu ya bar Najeriya ba saboda Oyegun ba

3. Akwai ci gaba a arewa

Yan arewa

Babu shakka mun ga ci gaba a Najeriya domin yanzu mutun na iya fita cikin kwanciyar hankali ba tare da fargaba ba, a da mutun na cikin gidansa amma yana zullumi domin za’a iya far masa a koda yaushe, amma a yanzu Alhamdulillah babu wannan. Kuma muna fatan Allah ubangiji ya ci gaba da kawo karshen ta’addanci a kasar tamu.

4. Buhari na bukatar Lokaci

Ya kamata muba gwamnatin shugaba Buhari dan lokacin, domin kar ku manta shima kansa shugaban kasa ya zo ya tarar da wasu abubuwa wanda daidaita su na bukatar dan lokaci. Zuwa yanzu dai muna saka ran cewa komai yazo karshe abubuwa sun kusa warwarewa da yardarm Allah. Kuma muna fatan Allah ya kari shugaban kasa da lafiya ya kuma tallafa masa a cikin manufofinsa na alkhairi a kan kasar.

The post Muhimman abubuwa 4 da wasu yan Arewa suka fada a kan Shugaba Buhari (Hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Muhimman abubuwa 4 da wasu yan Arewa suka fada a kan Shugaba Buhari (Hotuna)"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*