Matasan Yarbawa da Egun sunyi rikici a Legas

Rikicin da ya barke tsakanin matasan Yarbawa da na Egun ya janyo sanadiyar kona dakuna da gidaje da rumfuna kusan 200.

Jaridar Punch ta ruwaito mana cewa rikicin ya fara ruruwa ranar lahadi 6 ga watan Nuwamba inda Yarbawa suka ba yan Egun umurnin su tashi daga yankin, su kuma suka ki.

vllkyt6sqnrgtnnns.fe0e36db

Abubuwa sun baci ranar laraba 9 ga watan Nuwamba inda matasan Yarbawa suka hasa ma runfunan gurin wuta wanda shi ya kara hargitsin.

Wasu daga cikin matasan sun gudu,wasu kuma an bar su da rauni, wutar kuma ta cigaba da ci na wani lokaci.

vllkytjkss8f7jnqg.f4a7f718

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

Yan sanda daga yankin ofishin na Moroko an kira su dan kawo dauki, kuma an tabbatar da cewa an ceci wani yarinya.

Yace lokacin da aka banka ma gurin wuta mahaifan yarinyar sun guda sun barta, kukan yarinyar ya janyo hankalin yan sandan, inda suka shiga har dakin suka ceci yarinyar suka hada ta da mahaifanta.

Ba wanda aka kashe, mutane 3 dai sun samu rauni, gaba daya gurin an saka mai wuta.

vllkyt1o9g8jbcsfk8.b06cea7c

Wani wanda yake zaune a yankin mai suna Hansu” yace rikicin ya fara ranar laraba, wasu sun zo sun ce sun sayi gurin mu, sai suka ce mu tashi, ba mu san ricin ze kai haka ba, sai da matasan Yarbawa suka kutso a yankin ranar laraba in da suka saka ma yankin namu wuta, na rasa komai nawa,iyalina sun zama marasa muhalli.

The post Matasan Yarbawa da Egun sunyi rikici a Legas appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Matasan Yarbawa da Egun sunyi rikici a Legas"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*