Kamar Jonathan a 2011, Zanga-zangar adawa da Trump ta barke a Amurka

– Daruruwan mutane sun shiga zanga zangar adawa da zababben shugaban kasar Amurka, Donald Trump a sassa daban-daban na kasar, inda suka sha alwashin ci gaba da adawa da manufofin sa.

– A birnin Washington daruruwan masu zanga zangar suka taru a gaban fadar shugaban kasa, duk da sanyin da ake yi, inda suka bayyana Trump a matsayin mai nuna banbancin launin fata da cin zarafin mata da kuma raba kan al’umma.

Trump Protests

Trump Protests

Trump protests

Trump protests

trump protests 4

A birnin New York, masu zanga zangar sun kona tayun mota a Dandalin hadin kai, a Carlifornia daliban makarantu ne suka fice daga azuzuwa dan adawa da shugaban, a Los Angeles daruruwan matasa suka gudanar da gangami a Dakin taron birnin suna cewa su Trump fa ba shugaban su bane.

A Pennsylvania, daruruwan daliban jami’ar Pittsburg suka yi jerin gwano a titunan birnin, a Carlifornia kuma an raunana daya daga cikin masu zanga zangar.

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

KU KARANTA: Majalisar dattawa na shirin kunyata fadar shugaban kasa

A wani labarin kuma a nan gida Najeriya, Hukumar hana fasa kwabri ta Najeriya,Kwastam ta soma raba wasu kayakin da aka kama a hannun yan sumogal, ga al’ummomin da rikicin Boko Haram ya shafa a arewa maso gabashin Najeriya.

Dubban jama’a ne dai rikicin Boko Haram da aka shafe fiye da shekaru shida ana fama da shi,ya shafa,musamman a jihohin Adamawa,Borno da kuma jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya.

Wannan ne dai karon farko da hukumar ta kwastam ke raba wadannan kayakin tallafin da kanta a jihar Adamawa,daya daga cikin jihohin da rikicin Boko Haram ya shafa.

Kayakin sun hada da abinci,sutura da kuma sabulai,inda aka rabawa al’ummomin da rikicin Boko Haram ya shafa a kananan hukumomi bakwai da a baya suka fada hannun yan bindiga masu tada kayar bayan na Boko Haram,dama sansanonin yan gudun hijira dake jihar Adamawa.

Iya Abubakar shi ne mataimakin shugaban hukumar ta kwastam ,da ya wakilici shugaban hukumar,yace wadannan kayaki na ko cikin kayakin da hukumar ta kame,don haka ta kawo a rabawa wadanda rikicin ya shafa.

The post Kamar Jonathan a 2011, Zanga-zangar adawa da Trump ta barke a Amurka appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Kamar Jonathan a 2011, Zanga-zangar adawa da Trump ta barke a Amurka"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*