Hargitsi a Abuja yayinda masu zanga-zanga suka mammaye hekwatar INEC

A ranar Talata 8 ga watan Oktoba, yan zanga-zanga da dama sun mamaye hedkwatar hukumar zabe ta kasa (INEC) a Abuja, kan zargin an samar da sakamakon zabe na jabu a jihar Rivers.

Masu zanga-zanga sun mamaye Abuja

Ana zargin anyi amfani da takardun zabe na jabu a zaben Rivers

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa masu zanga-zangar na zargin cewa tsohuwar mukadaddashin hukumar ta INEC, Amina Zakari, tana hada kai da wasu yan siyasar jam’iyya mai ci suna buga takardan zabe na jabu. Ba a samar da hujja da zai tabbatar da zargin ba.

Sun bukaci mukaddashin INEC Mahmud Mohammed ya ajiye aiki, haka kuma Amina Zakari wacce a yanzu take kwamishina a hukumar INEC.

KU KARANTA KUMA: Kamanni guda 4 tsakanin zaben Najeriya da na Amurka

A makon da ya gabata, hukumar zaben ta saka ranar sake zaben jihar Rivers a ranar 10 ga watan Disamba don samar da dan majalisar da zai wakilci jihar kudu-maso-kudu a majalisar dattawa da majalisar wakilai.

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

A baya zaben cike kujerun ya zo da rikice rikice don haka hukumar zaben ta kasa ta daga zaben.

Yan siyasar da dama sun yi tsananin fushi a jihar Rivers bayan wani bidiyo ya fito wanda aka buga jabun takardun zaben da ba’a riga anyi ba na kujerar sanata.

An rahoto cewa yan sanda sun fasa wani abun buga takarda na jabu wanda ake buga takardun zabe na jabu a garin Port Harcourt a ranar Asabar, 5 ga watan Nuwamba.

A wata sanarwa da aka saka a yammaci ranar Lahadi, 6 ga watan Nuwamba da kuma sa hannun Prince Dayo Adeyeye, sakataren labaran jam’iyyar PDP ta kasa, jam’iyyar adawan sun yi kira ga daukar matakin gaggawa a bangaren shugaban kasa kan wadanda suke da hannu a ciki.

Sun kuma yi kira ga dakatar da ministan sufuri Chibuike Ameachi wanda aka rahoto cewa an ambace shi a masu nasaba da abun buga jabun sakamako.

The post Hargitsi a Abuja yayinda masu zanga-zanga suka mammaye hekwatar INEC appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Hargitsi a Abuja yayinda masu zanga-zanga suka mammaye hekwatar INEC"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*