Buhari ya nada dan-uwan Sarkin Ife a mukamin Jakada

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada dan uwan Sarkin Ife mai suna Yarima Abimbola Adegboyega Ogunwusi mukamin jakadan Najeriya.

Shugaba Buhari, Farfes Osinbajo da Sarkin Ife

Shugaba Buhari, Farfes Osinbajo da Sarkin Ife

Yarima Abimbola Adegboyega Ogunwusi, yaya ne ga Sarkin masarautar Ife Alayeluwa Oba Adeyeye Ogunwusi, Ojaja II, kuma shine wakilin jihar Osun a jerin sunayen jakadun da Shugaba Buhari ya aika ma majalisa.

Bugu da kari Yarima Abimbola Adegboyega Ogunwusi yana rike da sarautar gargajiya ta Sooko Laekun of Ile Ife, aikinsa a masarauta shine kula da juya akalar Yarimomin dake masarautar Ife.

Kafin nadin nasa a matsayin Sooko Laekun of Ile Ife, dan uwansa Yarima Dapo Sijuwade ne ke rike da mukamin, bayan rasuwar Yarima Dapo ne sai Sarkin Ife ya nada shi sarautar a ranar Asabar 8 ga watan Oktoba.

Yarima Abimbola Adegboyega Ogunwusi

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

Yarima Abimbola Adegboyega Ogunwusi

KU KARANTA: Dan yi ma kasa hidima ya rasu

Yarima Abimbola Adegboyega Ogunwusi yayi karatun digirinsa a jami’ar Ibadan, sa’annan hamshakin dan kasuwa ne wanda yayi fice a harkar siya da siyar da kadarori, harkar gine gine, Noma da hakar ma’adanai.

Yarima Abimbola Adegboyega Ogunwusi tsohon ma’aikacin bankin Access, daga bisani ya koma kasar waje da zama, sai a yanzu ne ya dawo ya cigaba da harkokin kasuwancinsa.

A wani labarin kuma, da dama daga cikin Sanatocin Najeriya sun ki amincewa da sunayen jakadun da shugaban kasa ya aike ma majalisar dattijai, sai dai shugaban majalisar Sanata Bukola Saraki yaki yarje musu.

The post Buhari ya nada dan-uwan Sarkin Ife a mukamin Jakada appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Buhari ya nada dan-uwan Sarkin Ife a mukamin Jakada"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*