Bayan lashe zaben shugaban kasa, jam’iyyar Trump ta sake samun wannan gagarumar nasarar (Karanta)

– Jam’iyyar Republican ta lashe zaben majalisar Wakilai tare da haramtawa Democrat karbe ragamar majalisar Wakilai a zaben Amurka da aka gudanar inda dan takarar Jam’iyyar Donald Trump ya lashe zaben shugaban kasa

– Republican ta samu rinjayen kujerun Majalisar Dattijai 54, yayin da 46 suka fada hannun ‘yan Democrat

Donald Trump in WWE

Donald Trump in WWE

A cikin sanarwar da ya fitar Shugaban Republican Reince Priebus ya ce wannan babbar nasara ce ga Jam’iyyar bayan sun lashe kujerar shugaban kasa tare da ci gaba da rike ragamar Majalisar Dattijai.

KU KARANTA KUMAKurkuku 5 masu hadarin gaske a Najeriya

Republican ta samu kujeru 239 a Majalisar Wakilai wanda ya ba Jam’iyyar ci gaba da jagoranci a Majalisar na tsawon shekaru shida. Democrat ta samu kujeru 196 ne a zaben.

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

Sakamakon zaben dai ya sabawa kuri’un jin ra’ayoyin jama’a da dama da kafofin yada labarai suka gudanar.

Rashin lashe Majalisar Dattijai dai baraka ce ga Democrat musamman wajen kokarin toshe wasu sabbin tsare tsaren shugaban kasa Donald Trump.

A wani labarin kuma a zauren majalisar tamu a nan Najeriya, Rahotanni daga majalisar Dattawa sun nuna cewa sanatoci na nazarin yin watsi da sunayen jakadun wucin gadi su 46 da shugaba Muhammad Buhari ya gabatar masu don neman amincewarsu.

Da yake karin haske kan batun, Mai Magana da yawun Majalisar, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya ce kwamitin majalisar kan Harkokin waje shi ya bayar da shawarar yin watsi da sunayen sakamakon korafe korafe da aka samu.

The post Bayan lashe zaben shugaban kasa, jam’iyyar Trump ta sake samun wannan gagarumar nasarar (Karanta) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Bayan lashe zaben shugaban kasa, jam’iyyar Trump ta sake samun wannan gagarumar nasarar (Karanta)"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*