Anyi taho mugama tsakanin Tireloli biyu

Mutane biyu ne suka rasa rayukansu a ranar Talata 8 ga watan Nuwamba bayan wata arangama daya faru tsakanin Tireloli guda biyu a kan babbar hanyar Lekki zuwa Epe na jihar Legas.

Hdarin

Hdarin

Rahotanni sun nuna cewa daya daga cikin Tirelolin na dauke da karafan rodi, shine ya afka ma dayar Tirelar dake dakon siminti. Jaridar Punch ta ruwaito cewar direban motar Tirelar dake dauke da karafan rodi mai suna Mubarak tare da yaron motarsa ne suka rasu yayin da karafan suka fado musu.

Manajan hukumar bada agajin gaggawa na jihar Legas (LASEMA) Adesina Tiamiyu yace hukumar ta isa inda hadarin ya afku, sai dai yace ko kafin su isa har mutanen biyu sun rasu.

KU KARANTA: Budurwa ta hallaka kanta kan saurayi

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

Bincike da hukumar ta gudanar ya bayyana cewa wata motar Tirela mai lamba AGL 86 XN dake dauke da karafan rodi tana tsananin gudu ce ta afka ma wata Tirela dake dauke da Siminti wadda take ajiye a gefen hanya, hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutane biyu. Jam’ai sun iya gano gawar Direban motar Mubarak da yaron motar mai suna Baki, inda aka ciro gawawwakin nasu aka mika su ga yansandan Elemoro, inda aka janye Tirelolin zuwa ofishin yansandan don cigaba da gudanar da bincike.” Inji Tiamiyu.

Tiamiyu yace hukumonin da abin ya shafa zau gudanar da sahihin bincike. Daga nan sai ya shawarci direbobi dasu dinga bin dokar hanya yayin da suke tuki, kuma su tabbatar da ajiye motocin da suka lalace a inda ya kamata don kiyaye sake faruwar irin wannan lamari a gaba.

A wani labara kuma, Tirelar NNPC mai lamba XKN 222 SA dauke da mai sama da lita 40,000 ta fada kan wata mota kirar marsandi a ranar Asabar inda ta kashe direban motar nan take. Tirelar na kan hanyar zuwa garin Owerri na jihar Imo ne yayin da hadarin ya faru.

The post Anyi taho mugama tsakanin Tireloli biyu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Anyi taho mugama tsakanin Tireloli biyu"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*