An fi ba musulmai da dabi’un musulunci fifiko a Najeriya, babban malamin coci ga Buhari

– Shugaban cocin Church of Nigeria in the Anglican Communion, Archbishop Nicholas Okoh bai ji dadi ba

– Rashin jin dadin nasa ya samo asali ne daga gaskiyar cewa ana ci gaba da kashe kiristoci a arewa

– babban malamin na kirista yayi kira ga Muhammadu Buhari da ya magance al’amarin

okoh da buhari

Archbishop Okoh tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban cocin Church of Nigeria in the Anglican Communion, Archbishop Nicholas Okoh ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya magance yawan satar mutane, tursasa mutane su musulunta da kuma auren dole da akeyi wa matan kiristoci a Arewa.

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

A cewar jaridar Leadership, musamman malamin cocin yayi kira ga shugaban kasa da ya yi gaggaan magance yawan kisan rashin aldalci da akeyiwa kiristoci a Arewa saboda rashin hakurin addini.

KU KARANTA KUMA: Kungiyoyin Mafarauta na samun horo kan Boko Haram

Archbishop Okoh yayi furucin ne a lokacin da yake Magana tare da yan jarida lokacin taron Divine Common Wealth Conference (DWCCON)  na shidda da akayi a Abuja.

Ya nuna fushinsa a kan shirun shugaban kasa kan raunanun abubuwan addini dake faruwa a kasar, ya bayyana cewa zai iya haifar da rashin kwanciyar hankali a kasar.

Furucin babban malamin na coci ya zo ne yan kwanaki kadan bayan babban kotun majistare ta dakatar da shari’a tare da wanke wasu matasan musulmai guda hudu da aka zarga da kashe Misis Bridget Agbahime mai shekaru 74 a ranar 2 ga watan Yuni, 2016 kan zargin cewa ta aikata sabo.

The post An fi ba musulmai da dabi’un musulunci fifiko a Najeriya, babban malamin coci ga Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "An fi ba musulmai da dabi’un musulunci fifiko a Najeriya, babban malamin coci ga Buhari"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*