Adalci ko rashin sa? Hukumar kwastam ta rabawa yan gudun hijira kayan da ta kwace (Hotuna)

-Hukumar hana fasa kwabri ta Najeriya, Kwastam ta soma raba wasu kayakin da aka kama a hannun yan sumogal, ga al’ummomin da rikicin Boko Haram ya shafa a arewa maso gabashin Najeriya.

-Dubban jama’a ne dai rikicin Boko Haram da aka shafe fiye da shekaru shida ana fama da shi,ya shafa,musamman a jihohin Adamawa,Borno da kuma jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya.

Hameed Ali

Shugaban hukumar kwastam, Hameed Ali

Buhari's customs bossCustoms 5

Wannan ne dai karon farko da hukumar ta kwastam ke raba wadannan kayakin tallafin da kanta a jihar Adamawa,daya daga cikin jihohin da rikicin Boko Haram ya shafa.

Kayakin sun hada da abinci,sutura da kuma sabulai,inda aka rabawa al’ummomin da rikicin Boko Haram ya shafa a kananan hukumomi bakwai da a baya suka fada hannun yan bindiga masu tada kayar bayan na Boko Haram,dama sansanonin yan gudun hijira dake jihar Adamawa.

Customs 2customsCustoms 1

Ku Karanta kuma: Ta’adancin yan Neja Delta ne yasa na kara farashin siminti na – Dangote

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

Iya Abubakar shi ne mataimakin shugaban hukumar ta kwastam ,da ya wakilici shugaban hukumar,yace wadannan kayaki na ko cikin kayakin da hukumar ta kame,don haka ta kawo a rabawa wadanda rikicin ya shafa.

Shiko Hon. Musa Ahmad Bello shugaban karamar hukumar Mubi ta Arewa,daya daga cikin yankunan da suka fada hannun yan Boko Haram,yace zasu yi adalci a rabon kayakin.

Suma dai shugabanin kungiyoyin addinin Musulunci da Kirista,sun gargadi jama’a da su yi gaskiya ayayin rabon kayakin tallafin.

Kimanin buhunan shinkafa 5,460 da sabulun wanka katon 78 da jarakunan man girki 600 ne hukumar kwastan din ta kawo domin rabawa al’ummomin da rikicin Boko Haram din ya shafa.

Haka zalika dai Rahotanni daga majalisar Dattawa sun nuna cewa sanatoci na nazarin yin watsi da sunayen jakadun wucin gadi su 46 da shugaba Muhammad Buhari ya gabatar masu don neman amincewarsu.

Da yake karin haske kan batun, Mai Magana da yawun Majalisar, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya ce kwamitin majalisar kan Harkokin waje shi ya bayar da shawarar yin watsi da sunayen sakamakon korafe korafe da aka samu.

The post Adalci ko rashin sa? Hukumar kwastam ta rabawa yan gudun hijira kayan da ta kwace (Hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Adalci ko rashin sa? Hukumar kwastam ta rabawa yan gudun hijira kayan da ta kwace (Hotuna)"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*