Yayan Sanata Kabiru Marafa sun rasu sanadiyyar hadarin mota

Yayan sanatan mai wakiltar mazaba Zamfara ta tsakiya a majalisar Dattijai Sanata Kabiru Marafa sun rasu ranar litinin 7 ga watan Nuwamba sakamakon wani mummunan hadari daya rutsa dasu.

Baru da Marafa

Baru da Marafa

Yaran su biyu da suka hada da Awwal da Maryam sun rasu ne sakamakon hadarin mota daya rutsa dasu a kan hanyar Dandotton Tsafe, yayin da suke kan hanyar dawowa Kaduna.

Shugaban hukumar tace albarkatun mai na kasa MK Baru ya tabbatar da rasuwar bayan ya kai ma sanatan ziyarar jajentawa, dama dai Marafa shine shugaban kwamitin majalisar dattijai dake kula da bangaren ma’adanan mai na kasa.

KU KARANTA: Dan bindiga ya kashe masu kallon kwallo 13

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

Baru ya bayyana rasuwar a matsayin wani hukunci da Allah Ya riga Ya tsara, sa’annan yayi addu’ar jinkai ga mamatan.

Sanata Marafa tare da tawagar shugaban NNPC

Sanata Marafa tare da tawagar shugaban NNPC

A wani labarin kuma, ita ma sanata Stella Oduah ta dawo bakin aiki bayan kwashe wata guda tana jimamin mutuwar danta Maxwell Chinedu Etoromi wanda ya rasu a asibitin Turkish dake Abuja a ranar Juma’a 26 ga watan Agusta.

The post Yayan Sanata Kabiru Marafa sun rasu sanadiyyar hadarin mota appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Yayan Sanata Kabiru Marafa sun rasu sanadiyyar hadarin mota"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*