Yadda Najeriya tayi barna da wasu Kudi lokacin PDP

– Sakataren Hukumar NEITI ya bayyana yadda gwamnatin baya suka yi facaka da wasu kudi masu yawan gaske

– Mista Waziri Adio yace Gwamnatin Obasanjo, Yaradua da na Jonathan sun yi barna da wasu kudi har Tiriliyan 70

– Shugaban NEITI yace wadannan kudi ne da aka samu wajen sayar da mai

Waziri Adio ya e Najeriya tayi barna

 

 

 

 

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

 

 

Mista Waziri Adio wanda shine Sakataren Hukumar NEITI ya bayyana yadda Gwamnatin baya a Kasar suka barnatar da wasu kudi masu shegen yawan gaske. Mista Adio yayi wannan bayani ne a Ranar Talata, 8 ga wata da yake magana da wasu ‘Yan Majalisar Dattawa na Kasar.

Waziri Adio yace a cikin shekaru 15, Najeriya tayi facaka da wasu kudi da suka wuce Naira Tiriliyan 70. Adio ya bayyanawa Kwamitin Majalisar Dattawa na Kasar da ke kula da ayukkan Gwamnati haka ne yayin da suka kawo masa ziyara Ofisihin sa.

KU KARANTA: Yadda IBB ya daure ni a Benin-Shugaba Buhari

Waziri Adio yace wadannan kudi ne da Najeriya ta samu daga fitar da mai cikin shekaru 15 na mulki; daga shekarar 1999 zuwa 2014. A wannan lokaci Janar Obasanjo da Marigayi Ummaru Yar’adua da kuma Dr. Goodluck Jonathan ne suka mulki Kasar a karkashin Jam’iyyar PDP. Waziri Adio ya bada shawara, yadda ba za a kara irin wannan barna ba..

A wata duniyar kuma, ana rikici tsakanin Ministar Kudi Kemi Adeosun da kuma Ministan Kasafi Udo Udoma. Hakan na iya jawo a samu bata lokaci wajen shirya kasafin kudin shekara mai zuwa.

The post Yadda Najeriya tayi barna da wasu Kudi lokacin PDP appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Yadda Najeriya tayi barna da wasu Kudi lokacin PDP"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*