Yadda na sa ‘ya ‘yana 14 fashi da makami –Tsohon barawo

-Wani tsoho mai shekara 75 ya bayyana yadda ya sa ‘ya ‘yansa 14 fashi da makami ta hanyar horas da su, da kuma fita aiki  a jihar Niger

– Shanjijiri Yahaya ya ce ya kai kimamin shekara 30 yana sata, da fashi da makami, da satar mutane, da satar dabbobi, amma ya tuba  

gunmen

Wani tsoho mai kimanin shekar 75 da haihuwa wanda kuma ya tuba da sata, ya bayyana yadda ya koyawa ‘ya ‘yansa su 14 na cikinsa, sata da fashi da makami .

Tsohon mai suna Yahaya Shanjijiri wanda ya tuba, ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da aka yi a jihar Niger, a inda masu aikata laifi kimanin 5,000 suka tuba a bainar jama’a ciki har da baturen ‘yan sanda na karamar hukumar Rijau.

Shanjijiri  wanda a da, kasurgumin barawo ne ya ce ya kai kimanin shekaru 30  yana sata da kuma aikata manyan laifuka, ya kuma ce, ya daina fita sata shekaru 8 da suka wuce, sai koma horas da ‘ya ‘yansa na cikinsa wannan sana’a.

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 6 na mamaki game da Kanar Abu Ali

Shanjijiri ya bayyana yadda ya soma sata da cewa, “Ban kai kimanin shekara 10 da haihuwa ba na soma sata, soma ne daga satar awaki a makwabta sai na koma satar shanu kafin in koma fashi da makami.”

“An kama ni, an kuma kai ni fursuna  sau 11, an kuma sake ni, na fi yin fashi a yakunan Sokoto, da  Kebbi da Niger, na kuma yi fashi sama da 300, kwatankwacin fashi sau 3 a wata daya.”

Dangane da abin da ya ke samu ya ce: “Ni da yarana wanda cikin har ‘ya ‘yana muna samun kimanin Naira miliyan 2 zuwa 3, muna kuma raba abin da muka samu gida hudu, a inda muke ware na  jami’an tsaro, da shari’a, da kuma bokaye da ‘yan tsibbu masu bamu sa’a, sauran kuma mu zuba a aljihu mu sha shagalinmu.”

Shanjijijri ya kuma ce su ne alhakkin yawancin fashi da makami, da satar shanu, da satar mutane da ake yi a jihohin Niger, da Sokoto, da Kebbi, sannan ya ce, su ba sa kisa a yayin sace-sacensu, ya kuma kara da cewa, babu wanda ya tilasta su tuba, sun yi ne don neman gafarar Ubangiji, kuma nemi gafarar duk wadanda suka yi wa sata a baya.

The post Yadda na sa ‘ya ‘yana 14 fashi da makami –Tsohon barawo appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Yadda na sa ‘ya ‘yana 14 fashi da makami –Tsohon barawo"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*