Ta kashe kanta sakamakon saurayinta ya yaudareta

Wata budurwa yar kasar Zimbabwe ta hallaka kanta bayan saurayinta dan Najeriya ya yaudareta, ya rabu da ita, bayan ya dibga mata ciki.

vllkyt4cit7h8rm3l.9df143a3

Elizabeth Choto

Budurwar mai shekaru 27 mai suna Elizabeth Choto dalibace a jami’ar Cyprus, an tsinci gawarta ta reto daga saman silin a dakinta dake rukunin dakunan kwanan yan mata na jami’ar, an ruwaito Choto ta kashe kanta ne bayan ta bayyana ma saurayinta zancen tana dauke da cikinsa, shi kuma sai ya rabu da ita, sakamakon hakan ta kashe kanta.

Hukumar jami’ar ta tabbatar da faruwar lamarin, ta wani sanarwa data fitar tana cewa “wata dalibar jami’ar Cyprus yar kasar Zimbabwe mai suna Elizabeth Choto ta hallaka kanta. Mun tabbatar da kasancewar dalibar tana zaune a dakunan kwanan na yan matan jami’ar A2 Block. Muna bukatan dalibai dasu kwantar da hankulansu yayin da bincike ke gudana don gano musabbabin mutuwarta.

KU KARANTA:Yadda mu ke yin fashi da makami

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

“a yanzu haka ana binciken gawar tata, kuma zuwa ranar sabar 5 ga watan Oktoba zamu fitar da sanarwar a hukumance dangane da abin da aka gano. Zamu cigaba da tuntuban ku.”

Elizabeth Choto

Elizabeth Choto

Wani dalibin makarantar daya bukace a sakaya sunansa ya tabbatar da maganan tana da ciki, inda yace amma saurayinta ya musanta cikin sa ne. “na san Choto, saboda muna cikin kungiya daya na yan kasar Zimbabwe, mu muka fara samun labarin mutuwarta” inji dalibin.

Dalibin ya cigaba da fadin “abinda ya faru shine ta samu matsala da saurayinta bayan ta bayyana masa tana da ciki. Nan da nan saurayin ya rabu da ita, kuma ya musanta ikirarin ta na cewa shine yayi mata ciki. Sai kawai ta kashe kanta.”

The post Ta kashe kanta sakamakon saurayinta ya yaudareta appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Ta kashe kanta sakamakon saurayinta ya yaudareta"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*