Mu shar: Ka ji uban kudin da Najeriya za ta samu?

– Gwamnatin Najeriya za ta karbi dala biliyan biyar

– Gwamnatin kasar za ta karbi wannan kudi ne daga Kamfunan mai

– Manyan Kamfunan mai na Kasar waje da ke Kasar ne za su ba Najeriya wannan makudan kudi

Ibe-Emmanuel-Kachikwu

 

 

 

 

 

 

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

 

 

Gwamnatin Najeriya za ta karbi Biliyan $5 daga Manyan Kamfunan mai da ke Kasar nan bisa yarjejeniyar da suka yi. Najeriya ta dade tana rigima da Kamfunan man wajen biyan wannan kudi. Sai dai kawo yanzu, an yi yarjejeniyar cewa Kasar za ta karbi wadannan kudi daga hannun Kamfunan Inji Jaridar Financial Times.

Wani Rahoto daga Jaridar ta Financial Times tace Gwamnatin Kasar ta amince ta karbi wadannan kudi daga hannun manyan Kamfanun mai da ke cikin Kasar. Ministan Fetur, Ibe Kachikwu ya bayyana haka kwanan nan. Kamfuna guda 5 biyar ne za su biya wannan kudi na yarjejeniyar da suka kulla da Kasar daga shekarar 2010 zuwa 2014.

KU KARANTA: OBA na BENIN ya yabawa Shugaba Buhari

Kamfunan man Kasar wajen da ke aiki a Kasar za su kuma so su cigaba da kasuwanci a Najeriya. Sai dai ana bukatar sa hannun Gwamnatin Tarayyar Kasar da kuma na Shugaban Kasa kafin an kammala wannan yarjejeniya.

Haka kuma, Mista Waziri Adio wanda shine Sakataren Hukumar NEITI ya bayyana yadda Gwamnatin baya a Kasar suka barnatar da wasu kudi masu shegen yawan gaske da suka kai Naira Tiriliyan 70 na man fetur. Kasar ta samu wannan kudi ne daga shekarar 1999 zuwa 2014.

 

The post Mu shar: Ka ji uban kudin da Najeriya za ta samu? appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Mu shar: Ka ji uban kudin da Najeriya za ta samu?"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*