Kamanni guda 4 tsakanin zaben Najeriya da na Amurka

Donald J Trump ya kasance shugaban kasar Amurka na 45. Ya kasance zazzafar yakin neman zabe a tsakanin Gilary Cliton da Donald Trump, kuma mutane da dama sunyi mamaki da jin sakamakon zaben.

Shugabannin kasa

Shugabannin kasa

A halin yanzu, fitaccen malamin kiristan Najeriya Temitope Joshua na cocin Synagogue Church of all Nations (SCOAN) a lokacin da yake huduba a cocinsa a ranar Lahadi, 6 ga watan Nuwamba, ya fadi cewa Hilary Clinton ce zata lashe zabe. Yana fuskantar suka mai tsanani saboda wannan.

Ga wasu daga cikin kamannin dake tsakanin zaben Najeriya na 2015 da kuma na Amurna na 2016:

1. Kiran waya

A lokacin da Donald Trump ke tazara a zaben shugabancin kasar, Hilary Clinton ta kira shi, ta yarda tare da taya shi murna. Wannan na kama da yunkurin da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi wanda mutane da dama suka yaba mai a kan haka.

Da aka kirga sakamakon zabe na daya daga cikin jihohi 36 na kasar Najeriya, kuma ya nuna kuru-kuru cewa dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, Muhammadu Buhari, ke jagotra, Jonathan ya kira Buhari don yarda da kayen.

Tsohon shugaban kasa Jonathan ya yi kiran da misalign karfe 5 na yamma a ranar Litinin, 30 ga watan Maris na shekara 2015 bayan ya ga cewa jam’iyyarsa ta sha kashi.

2. Shekaru

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

Wani bambanci shine shekarun shugabannin Najeriyan guda biyu da kuma na kasar Amurka. Yawancin yan adawan shugaban kasa Muhammadu Buhari sunyi amfani da damar shekarunsa a matsayin dalilinsu na kin goyon bayan sa.

Abun mamaki dukkansu biyu Buhari da Donald Trump na tsakanun shekaru 70s, shugaban kasa Buhari na da shekaru 73, yayinda aka haifi Donald Trump a ranar 14 ga watan Yuni na shekara 1946, don haka yana da shekaru 70.

KU KARANTA KUMA: Ango Abdullahi ya zargi Buhari da rashin kishin arewa

3. Ban mamaki

Kimanin mako daya da ya wuce, mutane da dama na ganin nasarar zaben Donald Trump a matsayin ba mai yiwuwa ba a gurare da dama a fadin duniya.

A yau mutane da dama suna cike da al’ajabin cewa Hilary Clinton ta sha kaye yayinda Donald Trump yayi nasara an gano haka ne ta yanda mutane ke Magana a gurare daban daban. Irin wannan mamakin ne a fuskokin yan Najeriya a shekara ta 2015.

4. Ta’addanci

Wani kamanni shine dandamali wanda dukkan shugaban kasa Buhari da shugaban kasar da aka zaba sukayi idan sun hau kujerar mulki da kuma alkawaran da sukayi. Annobar Boko Haram na daya daga cikin abubuwan da suka sace gwiwar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da kuma lokacin da Buhari yayi alkawarin kawo karshen su, ya samu goyon bayan mutane da dama.

A irin haka, yan ta’addan ISIS na daya daga cikin abunda Donald Trump yayi alkawarin kawar wa kuma babu makawa wannan na daga cikin hujojji masu karfi da ya bashi damar lashe zabe a dukkan mazabu.

The post Kamanni guda 4 tsakanin zaben Najeriya da na Amurka appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Kamanni guda 4 tsakanin zaben Najeriya da na Amurka"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*