Jam’iyyar PDP na kokarin dawowa mulki a 2019

Jam’iyyar PDP na kokarin hadewa da sauran wasu Jam’iyyun adawa na Kasar

Shugaban Bangaren Jam’iyyar PDP Ahmad Makarfi ya kafa wani kwamiti da zai duba wannan hadaka

Jam’iyyar PDP na kokarin karbe mulki daga hannun Jam’iyyar APC-mai mulki

Senator Ahmed Makarfi

Ahmed Makarfi na Jam’iyyar PDP

 

 

 

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

 

Jam’iyyar PDP mai adawa, na kokarin ganin ta karbe mulkin Kasar nan daga hannun APC zuwa shekarar zabe 2019. Shugaban wani Bangaren na PDP, Ahmed Makarfi ya nada wani Kwamiti da zai fara wannan shiri.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Ahmad Makarfi ya nada wani kwamiti mai dauke da mutane 115 da za su zauna suyi aiki da sauran Jam’iyyun adawa na Kasar wajen ganin sun karbe mulki daga hannun Jam’iyyar APC. Ahmad Makarfi yace sun fara shirin ganin cewa sun dawo mulki nan da zabe mai zuwa.

KU KARANTA: APC na kokarin hada kai da INEC – PDP

Ahmad Makarfi yace Kwamitin tayi kokarin bin duk hanyar da ta dace na hada kai da sauran Jama’a wajen dawowa mulkin Kasar domin ceto Najeriya da Damokaradiyya. Jam’iyyar PDP tace za tayi garambawul ga tsarin mulkin ta wajen ganin an ci wannan manufa.

An dai nada tsohon Ministan yada labarai na Kasar, Farfesa Jerry Gana ne a matsayin Shugaban Kwamitin. Jam’iyyar PDP tace lokaci fa na tafiya, don haka sai an dage. Jam’iyyar PDP, watakila ta hada kai da sauran Jam’iyyu kamar yadda APC mai mulki tayi a baya wajen buge PDP daga mulkin Kasar bayan shekara da shekaru tana mulkin Kasar.

The post Jam’iyyar PDP na kokarin dawowa mulki a 2019 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Jam’iyyar PDP na kokarin dawowa mulki a 2019"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*