Hanyoyi 6 da mulkin Trump zai taba rayuwar ‘yan Najeria

Karshen tika-tika, Tik, in ji masu iya magana, domin Donald Trump da ake ta fargabar hawansa mulkin Amurka ya lashe zabe, ko menene tasirin hakan ga ‘yan Najeriya wadanda ke gida da kuma na  Amurka? Ga dai wasu hasashe guda shida

Donald Trump

Donald Trump

Wariyar al’umma

A yakin neman zabensa Trump ya yi kira da wariyar al’umma musamman ga bakake da kuma Musulmai, Trump ya sha alwashin korar baki, tare da hana musulmai shiga kasar, kuma yawancin ‘yan Najeriya Musulmai ne.

Tsaurara dokokin shige da ficen kasar

Idan na zama shugaban kasa, duk zan kora su gida, zan kuma gina katanga a gabar teku (domin han shigowa).

Idan kai dan Najeriya ne, kana kuma sha’awar shiga Amurka ta baruniyar hanya to ka makaro, domin kida ya canza…

Tsanarsa ga Musulmai

Trump ya nuna tsanarsa a fili ga wadanda ke son kafa wata sabuwar daula da sunan musulunci mai aiki shari’a zalla, a kuma kan kowa da kowa, inda za ‘a rika hallaka Kristoci da kuma wadanda ba sa bin sunna. Trump ya ce ba zai lamunta ba. Ga ‘yan Najeriya Karshen Boko Haram ya zo.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasan Rasha,Vladimir Putin ya taya Trump murna

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

‘Yan luwadi sun shiga uku

Donald Trump ya kasance mai adawa da auren jinsi, ya kuma ce idan aka zabe shi, zai ga bayan wannan neman maza.

Ya ce: “Na tsane shi (auren jinsi). Ni dan garagajiya ne, duk da cewa ina da abokai da ke neman maza, ni na dauri ne.”

Ga ‘yan Najeriya wadanda ke zaune a Amurka wannan abin farin ciki ne, ba kamar Obama ba da ya goyi da bayan sha’anin a kuma hukumance.

Tsoron korar baki

A wani bincike da aka gudanar kan mazauna Amurka a shekarar 2006, Najeriya ce ke da yawan mutane a kasar, yanzu babu mamaki hankalinsu ya tashi na ganin cewa Trump zai yi musu diban Karen mahaukaciya da kora.

Amurka ta Amurkawa ce

A jawabinsa kan manufofin gwamantinsa kan harkokin kasashen waje a yayin yakin neman zabe a 27 ga watan Afrilu, Trump ya jaddada akidarsa ta cewa, Amurka ta Amurkawa ce. Kuma wannan da alamu shi zai ja akalar gwamnatinsa.

Ana jin Trump zai dauki kwakkwaran mataki kan bakin haure, da kuma bude sabo shafi a kan batun tsaro da kuma kawancen da sauran kasashe kan hakan.

The post Hanyoyi 6 da mulkin Trump zai taba rayuwar ‘yan Najeria appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Hanyoyi 6 da mulkin Trump zai taba rayuwar ‘yan Najeria"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*