Daki-daki: Yadda zaben kasar Amurka ya wakana

– Jiya Talata ne Amurkawa suka je rumfunan zabe a fadin kasar don zaben sabon ko sabuwar shugaban kasa.

– Biyo bayan yakin neman zabe mai tsawo, mai zafi kuma da ‘yan takarar neman shugabancin Amurka sukayi, yar takarar jam’iyyar Democrat Hillary Clinton da Donald trump na jam’iyyar Republican sun yi kira na karshe ga magoya bayansu.

clinton3

Clinton ta kira wannan zaben a matsayin babban gwaji, yayinda shi kuma Trump ya ayyana ranar a matsayin ta samun ‘yanci. Dukkansu sunyi bayani a safiyar yau Talata, ranar da ta zamo ta karshe wajen yakin neman zaben su, mai cike da abubuwan kuma tun daga daren jiya.

Ku Karanta kuma: Karanta yadda zaben Amurka ya banbanta da na Najeriya

A lokacin da suke gudanar da tarurrukan, Clinton a jihar North Carolina shi kuma Trump a jihar Michigan, aka sami sakamako daga kuri’un farko da aka kada a rumfunan zabe. Clinton ta sami yawancin kuri’un da aka kada a garin Dixville Notch dake jihar New Hampshire, inda ta sami galaba akan trump da kuri’u 4 shi kuma yana da 2.

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

An ga dogayen layuyyuka a safiyar yau a wurare kamar Virginia da New York a lokacin da aka bude rumfunan zabe.

A wani labarin kuma A yayin da Amurkawa ke fitowa kwansu da kwarkwatarsu domin kada kuri’un zaben sabo ko sabuwar shugaban kasa, mai cike da dinbin tarihi.

Wannan dai shine karon farko da aka taba samun mace ta zama ‘yar takarar babbar jami’iyar daya daga cikin jam’iyyun Amurka. Haka kuma an sami hamshakin mai kudi da bai taba rike kowanne irin mukamin siyasa ba, ya tsaya a matsayin dan takarar babbar jam’iyya.

Majiyar mu ta zagaya runfunan zabe a karamar hukumar Indiana, domin ganin abubuwan da ke faruwa, kasancewar jihar Pennslvania na daya daga cikin jahohin da suke da matukar muhimanci a zaben kasar Amurka.

Hasashe dai ya nuna babu wani dan takara da zai iya lashe zaben kasar ba tare da ya samu nasara a jihar Pennsylvania. Tun daga karfe 8 na safiyar yau Talata mutane ke ta fitowa maza da mata yara da manya don kada kuri’un su. Yawancin mutanen da Yusuf ya zanta da su sun bayyana cewa wannan zabe ne mai cike da dinbin tarihi. Ana sa ran ka kimanin karfe Goma na dare za a fara samun sakamakon zabe.

The post Daki-daki: Yadda zaben kasar Amurka ya wakana appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Daki-daki: Yadda zaben kasar Amurka ya wakana"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*