Alkawarurruka 10 na sabon shugaban Amurka a ofis

Hamshakin attajirin dan kasuwa dan kasuwa Donald Trump ya zama shugaban Amurka na 45, a wani jawabi da yayi na murnar cin zabe, ya yi wasu alkawarurruka 10 a ranarsa ta farko kan karagar mulki

Trump

Jim kadan da bayar da sanarwar lashen zabensa, dan shekara 70 da hahuwa Trump ya yi wani jawabin nasara cin zabe da kuma zama shugaba mai-jiran-gado  birnin New York, a inda ya dau wasu alkawuran yin wasu abubuwa a ranarsa ta farko a mulki kamara haka

1. Tattaro manyan janar-janar na sojin kasar tare da ba su umarnin kwanaki 30 su kawo karshen kungiyar ISIS.

2. Sake duba tsarin lafiya na Obamacare, da kuma soke wasu umarnin da Obama ya bayar a matsayinsa na shugaba mai cikakkaken iko.

3. Cikin gaggawa soma korar bakin haure masu aikata muggan laifi daga kasar.

4. Sanar da duk kasashen da suka ki karbar irin wadannan bakin haure masu laifi cewar, zan hana ‘yan kasar izinin shiga Amurka.

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

5. Gyara a ma’aikatar kula da tsaffin sojojin kasar.

6. Sanar da duk manyan shugabannin kamfanonin da ke shirin komawa kasashen waje cewa, za su biya harajin kashi 35.

7. Za mu sanar da sauran da kasashen da mu ke ba kariya cewa… ku yi hakuri muna son mu cigaba da kare ku, amma ba kwa yin abin da     ya dace, domin ba sa biya abin da ya kamata –dan kalilan.

8. Soma kula da sojoji.

9. Jingine tsarin sake tsugunnar da ‘yan gudun hijirar kasar Siriya .

10. Ganawa da jami’an kula da tsaron cikin gida da kuma janar-janar na soja don soma daukan matakan tsare kan iyakanmu daga kudanci.

 

The post Alkawarurruka 10 na sabon shugaban Amurka a ofis appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "Alkawarurruka 10 na sabon shugaban Amurka a ofis"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*