LABARI DA DUMI-DUMI: INEC: Ana zanga-zanga a garin Abuja

Ana zanga-zanga a Birnin Abuja yanzu haka saboda zaben Jihar Ribas

A yau Talata, 8 ga wata masu zanga-zanga suka burma Birnin-Tarayya Garin Abuja

Ana zargi Hukumar zabe za ta bada sakamakon bogi a zaben Jihar Ribas

INEC

 

 

 

googletag.cmd.push(function () {
googletag.display(“div-gpt-ad-1466009690089-0”)
});

Ana zanga-zanga a garin Abuja yanzu haka dalilin zaben Jihar Ribas. Jaridar Premium Times ta rahoto cewa masu zanga-zanga sun dura Birnin Tarayya harin Abuja da zargin Hukumar zabe ta INEC za ta fitar da sakamakon bogi a zaben Jihar Ribas da za a gudanar kwanan nan.

Ana ta yada cewa Hukumar zabe ta INEC za ta fitar da sakamakon karya na jabu a zaben Ribas da za a karasa kwanan nan. Ana cewa Kwamishinar zabe ta INEC, Aisha Zakari tana kokarin hada kai da ‘Yan siyasar APC masu mulki wajen yin magude a zaben da za a gudanar.

KU KARANTA: Mai ba APC shawara yayi murabus, ko meyasa?

Ana dai zargin Aisha Zakari da yunkurin hada kai da ‘Yan siyasar Kasar na Jam’iyyar APC mai mulki wajen fitar da takardun zabe na jabu, sai dai babu wata hujja da ke gaskata wannan zargin na su. Masu zanga-zanga suna kira da a tsige Kwamishinar Hukumar zaben watau Aisha Zakari.

A makon jiya ne dai Hukumar zabe ta Kasa watau INEC ta sa ranar 10 ga watan Disamba a matsayin ranar da za a karasa ragowar zaben ‘Yan Majalisun da suka rage a Jihar Ribas. An ta kokarin gudanar da zaben a baya, sai dai ko yaushe, sai da rigima ake karewa.

The post LABARI DA DUMI-DUMI: INEC: Ana zanga-zanga a garin Abuja appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Source: New feed

About the Author

kellhub
Kelly is a shy and lifestyle blogger addicted to new things, a die hard ManUtd fan, loves music and a good dancer but also a terrible singer .......winks.........

Be the first to comment on "LABARI DA DUMI-DUMI: INEC: Ana zanga-zanga a garin Abuja"

Leave a comment

Your email address will not be published.


*